IQNA

23:36 - November 29, 2016
Lambar Labari: 3480983
Bangaren kasa da kasa, miliyoyin masoya manzon Allah (SW) da iyalan gidansa tsarkaka sun nufi birnin Najaf na Iraki domin tunawa da wafatinsa da na jikansa Imam Hassan Mujtaba (AS) a hubbaren Imam Ali (S).

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, miliyoyin muuslmi ne suke yin tattaki zuwa hubbaren Amirul muminin (AS) da ke birnin Najaf domin halatatr tarukan tunawa da wafatin manzon tsira (SAW) da kuma jikansa Imam Hassan mujtaba (AS) da ake gudanarwa a wannan lokaci.

Tawagogin suna fitowa ne daga hanyoyi daban-daban da suke isa birnin najaf mai alfarma, inda a nan hubbaren mai tsarki na Amirul muminin yake.

Akwai dubban mutane da suke a kan hanaya suna yin hidima ga masu gudanar da wannan tattaki omin nuna alhihin wafatin manzon Allah da Imam Hassan Mujtaba.

Bisa ga kididdigar alkalumman da aka bayar an bayyana cewa adadin masu ziyarar zai kai kimanin mutane miliyan 3 a wannan shekara da ke gudanar da tarukan a birnin najaf.

3549704


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: