IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani A Jamai’ar Michigan Amurka Kan Muslunci

23:05 - December 03, 2016
Lambar Labari: 3481000
Bangaren kasa da kasa, daliban jami’a musulmi a birnin Dirbon na jahar Michigan ta kasar Amurka za su shirya gudanar da wani taron karawa juna sani da wayar da kai kan addinin mulsunci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na yanar gizo na «michiganjournal» cewa, taron za a fara shi ne daga ranar Litinin mai zuwa a jami’ar Michigan.

Babbar manufar gudanar da wannan taron karawa juna sani da wayar da kai kan mulsunci ita ce bayyana wa wadanda ba musulmi hakikanin koyarwar addinin muslunci, sabanin abin da suke tunani kan muslunci da musulmi.

A kan hakan taron zai samu halartar musulmi da ma wadanda ba musulmi, kuma masana za su gabatar da jawabai da kasidu kan mauduai daban-daban, wadanda suke nuni da cewa musulunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addini, da kuma girmama dan adam.

Daga cikin abin da shirin zai kunsa kuwa har da amsa tambayoyin Amurkawa da suke bukatar Karin bayani kan wasu lamurra da suka shafi addinin muslunci, bayanan kuma za a bayar da abinci ga dukkanin mahalarta a lokutan gudanar da taron.

Birnin Dirbon dai dai yana daga cikin birane da ke da yawan muuslmi a cikin biranan kasar Amurka, kuma wannan mataki ya zo biiyo bayan wata barazana da wasu mau kyamar musulunci suka yia cikin wannan mako a kan musulmin jahar da ma sauran musulmin Amurka.

3550212

captcha