IQNA

An Bude Baje Kolin Dadaddun Littafan Musulunci A Spain

22:19 - December 04, 2016
Lambar Labari: 3481001
Bangaren kasa da kasa, an budfe wani babban baje koli na tsoffin littafai na muslucni a karkashin shirin kungiyar ISESCO a garin Granada na kasar Spain.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya habarta cewa, kungiyar bunkasa al'adun muslunci ta ISESCO ta bude taron baje kolin ne a yankin Granada da ke cikin yankin Andalus a cikin kasar Spain.

Ana gudanar da baje kolin ne a ginin cibiyar bunkasa alaka ta nahiyar turai da larabawa a birnin na Granada tare da hadin gwiwa da ofishin jakadancin kasar Slovakia a kasar ta Sapain.

Daga cikin abubuwan da ake nunawa a wannan baje koli kuwa har da wasu daga cikin tsoffin littafai nan a addini daga kasar ta Slovakia.

Abdussamad Atonio Romiro masanin tarihi da al'adu kuma fitaccen marubuci a duniya, yan adaga cikin masu halartar wannan taro bisa gayyatar kungiyar bunkasa al'adun muslunci ta ISESCO wanda ta shirya domin kara fito da al'adun muslunci.

3550768


captcha