IQNA

An Samu Dadaddun Littafai Kan Ilmomin Kur’ani A Masar

23:24 - December 05, 2016
Lambar Labari: 3481004
Bangaren kasa da kasa, Muhammad sha’alan ya ce an samu wasu dadaddun littafai da aka rubuta kan ilmomin kur’ani a masalalcin Mukarram a cikin lardin Buhaira a Masar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yam sabi cewa, Muhammad sha’alan wakilin ma’aikatar kula da harkokin adini a lardin Buharai Masar ya ce an samu wasu littafai da aka rubuta kan ilmomin kur’ani a masalalcin Mukarram da ke lardin.

Ya ci gaba da cewa wadannan littafai da aka samu suna komawa zuwa ga shekaru masu yawa a baya, kuma an rubuta su a kan ilmomin da suka danganci kur’ani, wadanda ba kasafai ake samunsu ba yanzu ba, domin manyan malamai da aka yi a kasar ne a baya suka rubuta su.

Yanzu haka dai an kafa wani kwamiti wanda yake bin masallatai da kuma dakunan karatu domin gano irin wadanann littafai masu kima, wadanda suke da matsayi na musamman ta fuskar tarihi ga kasar ta Masar da kuma addinin muslunci.

Kwamitin dai ya hada da malamai da kuma masana kan harkokin tarihi, wadanda suke gudanar da ayyukan nasu karkashin sanya ido na ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

Littafan da aka samu a masalacin Mukaram dai sun hada da littafan bayanai kan ilmomin kur’ani da kuma tafsirinsa, gami da yadda ake tantance bayanai da suka shafi ayoyi da dalilan safkarsu, da dai sauran ilmomin da suka shafi wannan bangare.

3551110


An Samu Dadaddun Littafai Kan Ilmomin Kur’ani A Masar

An Samu Dadaddun Littafai Kan Ilmomin Kur’ani A Masar

An Samu Dadaddun Littafai Kan Ilmomin Kur’ani A Masar

An Samu Dadaddun Littafai Kan Ilmomin Kur’ani A Masar
captcha