Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na fortune.com cewa, kamfanonin na yanar gizo bas u cewa komai kan yuwuwar yin aiki tare da Trump wajen bin diidigin muuslmi ta hanyar yanar gizo.
A lokacin da yake yakin neman zabe Trump ya bayyana cewa idan har ya lashe zaben zai yi aiki tare da kamfaonin yanar gizo wajen bin diddigin masu yin hijira zuwa Amurka, domin gano musulmi daga cikinsu.
Wadannan kamfanoni dai ba su komai ba bayan da ya ci zaben, kan ko za su yi aiki tare da shi a kan wannan manufa tasa a kan musulmi ko kuma ba za su yi ba.
Trump dai yana daga cikin Amurka da suka shahara wajen kin baki yan kasashen ketare musamamn ma musulmi daga cikinsu, wadanda suke yin gudun hijira daga kasashensu zuwa Amurka, a lokacin yakin neman zabensa ya sha nanata cewa zai kori baki haure musamman musulmi, ku zai hana su shiga cikin Amurka.
Zabababen shugaban na Amurka dai ba zai iya yin wannan aiki ba dole sai hadin gwaiwa da manyan kamfanonin da suke samar da yanar gizo, wadanda kuma dukkaninsu na kasar Amurka ne.