Wannan taron dai zai samu halartar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke zaune a birnin, kamar dai yadda aka saba yi a kowace shekara.
Ayatollah Ramezani babban daraktan cibiyar na daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a wurin kan wannan rana mai albarka da kuma matsayin ma'abucin ranar amincin Allah ya tabbata a gare shi.
Gobe ne 9 ga watan Rabiul awwal ranar da limancin limamin karshe na iyalan gidan manzon Allah ya fara, wanda kuma wannan ran ace mai matukar muhimamnci mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allaha duniya baki daya.