IQNA

Sallar Hadin kai Tsakanin ‘Yan Sunna Da ‘Yan Shi’a A Taron Hadin Kai

23:07 - December 15, 2016
Lambar Labari: 3481037
Bangren kasa da kasa, an gudanar da sallar zuhur a taron makon hadin kai wadda dukkanin bangarorin muuslmi na sunna da shi da aka ayyata suka halarta.

Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, wannan salal da aka gudanar babban malamin addini na kasar Syria kuma mai bayar da fatawa Sheikh Badruddin Hassun ne ya jagoranci sallar.

Manayna malamai da masana na shi’a da sunna da suke halartar taron duk sun hadu a cikin sahu guda wajen salar hadin kai a taron makon hadin kai da ke gudana a Tehran.

Wannan ya zama babban abin buga misali wajen hada kan dukkanin al’ummar musulmi da ke da mahanga daban-daban a kan lamurra da suka shafi wasu bangarori na addini, amma sun hadu a kana bin da ya hada su baki daya shi ne musulmi.

A yau ne aka bude babban taron makon hadin kai na al’ummar musulmi karo na 30 a birinin Tehran na kasar Iran, tare da halartar shugaban kasar Hassan rauhani da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar.

3554216


captcha