Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alsharq ta kasar Qatar cewa, cibiyar ayyukan alkhairi Raf ce ta dauki nauyin raba wadannan kur’anai a garin Luga.
Baynain ya ci gaba da cewa, Sayyid Ali Badr Jub daga cikin amnyan jami’an yankin ya bayyana cewa, hakika wannan aiki na alhairi zai taimaka matuka wajen samar da karuwar ilimin kur’ani a yankin nasu.
Sayyid Mustafa Lauh, wanda shi ma daya ne daga cikin malaman addini na yankin, kuma shi ne wakilin dukkanin makarantun kur’ani na yankin a wajen karbar wannan kyauta, ya kuma bayyana cewa za su raba su ga dukkanin makarantun kur’ani na yankin baki daya.
Sayyid Mukhtar Fal, wanda shi ne shugaban kungiyar ayyukan alkhairi ta kasar Senegal ya bayyana cewa, hakika wannan aiki yana babbar kima a wajen al’ummar kasar Senegal baki daya, kuma hakan ya kara tabbatar da cewakasar tana kara samun ci gaba ta fuskar karatun kur’ani mai tsarki, tunda har ya zama ana da bkatuwa da dubban kwafin kur’ani mai tsarki a makarantu.