IQNA

An Girmama Wadanda Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur’ani Ta Mauritania

21:40 - December 28, 2016
Lambar Labari: 3481076
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron girmma makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da suka nuna kwazoa gasar kur’ani ta kasar karo na biya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Mauritaniya cewa, an gudanar da wannan taro ne tare da halartar malamai da masana gami da jami’an gwamnati na kasar.

Babban manufar taron ita ce girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar kur’ani ta kasa da aka gudanar a karo na biyar, inda aka mika kyautuka ga wadanda suka zo na daya, da na biyu da kuma na uku.

Khatari Mukhtar Sheikh Ali shi ne ya zo na daya a gasar, ya kuma samu kyautar kwafin kur’ani da kudi Aguya miliyan uku.

Sai kuma Ajiya Wuld Babah wanda ya zo a matsayi na biyu, ya samu kyautar mujalladin kur’ani guda da kuma Aguya miliyan biyu.

Sai kuma mata biyu da suka zo matsayi na uku tare, wato Rukayyah bint Muhammad da kuma Bilkis Bint Abdullah, inda suka samu kyautuka na kwafin kur’ani da kuma kudi miliya daya kowace daga cikinsu.

3557393


captcha