IQNA

Taron Tunawa Da Cika Shekara Guda Da Shahadar Ayatollah Nimr

22:50 - December 31, 2016
Lambar Labari: 3481085
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taroa birnin berlin na kasar Jamus domin tunawa da cika shekara guda da shahadar Ayatollah Baqir Nimr.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin Bahrain yau cewa, a ranar Talata mai zuwa 3 ga watan janairu, za a gudanar da zaman taro na tunawa da shahadar Ayatollah Nimr a cibiyar muslucni da ke birnin Berlin.

Bayanin ya ce taron zai hada da shirye-shirye masu yawa, da ahakan ya hada da addu'a ga malamin da sauran mutanen da Saudiyya ta kasha bisa zalunci, kan Allah ya akrbe su a matsayin wadanda suka yi shahada wajen fadin gaskiya ga azzaluman sarakunan.

Haka nan kuma akwai jawabai da az a gudanar, da suka hada bayni kan wannan malami bawan Allah, wanda ya karar da rayuwarsa wajen hidima ga al'ummarsa, wanda baya son zalunci a kansa kamar yadda kuma baya son zalunci a kan wani.

Masana da kumalamai za su halarci wurin, domin gabatar da kasidu kan Ayatollah Nimr, musamman ma wadanda sukan shi kuma suka yi rayuwa tare da shi, da kuma wadanda suka san shi ta hanyar karanta dimbin littafan addini da ya rubuta a bangarorin ilimomin addinin muslunci.

Hak anan kuma za a nuna wasu daga cikin hotunan da ke tabbatar da halin zalunci da danniya da al'ummar yankunan gabashin saudiyya suke fuskanta, sboda dalilai na banbancin mazhaba ko fahimta, wadanda kuma kasar ta dogara da dimbin arzikin da Allah ya huwace wa yankin nasu na danyen amn fetur da kuma iskar gas, amma suna rayuwa a cikin kunci da talauci, sakamakon miliin zalunci da kama karya da masautar kasar ke yi a knsu.

3557958


captcha