Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Nyasa Times cewa, Sheikh Muhammad Abdulhamid Silika shugaban majalisar malaman musulmia kasar Malawi ya bayyana cewa, bayan kwashe tsawon shekaru 10 yana tarjama, daga karshe dai ya samu nasarar kammala tarjamar kur’ani a cikin yau.
Bayan kammala wannan tarjama an kwashe tsawon watanni 6 a jere wani kwamitin malamai 14 daga kasar Malaysia suna gudanar bincike kan tarjamar da kuma bin diddikinta, bayan da suka amince da ita an buga kwafi dubu 20 na kur’ani da aka tarjama.
Shugaban kasar ne mutum na farko da ya fara sayen kwafi 200, inda ya raba shi ga mata da ska halarci taron kaddamar da wannan kwafin kur’ani.
Kimanin kashi 60 zuwa 70 na musulmin kasar Malawi suna Magana ne da harshen Yau, wanda hakan ya sanya wannan tarjama ta zama mai matukar amfani a gare su.
Kimanin kashi 36 na mutanen kasar Malawi miliyan 16 musulmi ne, kuma ana Magana da wannan harshe a kasashen Muzanbik da Tanzania.