IQNA

21:43 - January 02, 2017
Lambar Labari: 3481093
Bangaren kasa da kasa, harkar muslunci a Najeriya ta bukaci shugaban Najeriya da ya saki jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalato daga jaridar Guardian da ake bugawa a Najeriya cewa, kakakin kungiyar ta harkar musulmi a Najeriya, Ibrahim Musa, da ya ke maida martani akan jawabin shugaban kasar Muhammadu Buhari dangane da sakon sabuwar shekara, ya bukaci shugaban kasar da ya yi aiki da umarnin kotu na sakin Sheikh Ibrahim El-zakzaky.

Bugu da kari, Ibrahim Musa ya bukaci ganin shugaban kasar ta Najeriya ya sa an binciki kisan da aka yi wa mambobin harkar ta musulunci.

Kamar yadda kuma ya bayyana cewa a kowane llokaci suna gudanar da lamurransu lami lafiya, ba tare da wani abu ya taba faruwa ba, amma idan jami'an tsaro suka afka musu sai a bayyana hakan da cewa su ne suka tayar da hankali.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da dama sun bukaci gwamnatin ta Najeriya da ta saki sheikh Ibrahim Zakzaky ba tare da wani bat alokaci ba, amma dai har yanzu ana ci gaba da tsare a wani wuri da ba a sani ba, bayan dauke shi daga wurin da jami'an tsaron farin kaya suka yi a baya a wani wuri a birnin Abuja.

Daruruwan mutane ne dai sojojin kasar su ka kashe a harin da su ka kai a Husaniyar Bakiyyatullah a 2015 da kuma gidan Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky.

3558753


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: