IQNA

Tunawa Da Shahadar Ayatollah Baqir Nimr A Azarbaijan

22:29 - January 04, 2017
Lambar Labari: 3481099
Bangaren kasa da kasa, Jam'iyyar Islamic Party ta kasar Azarbaijan, ta fitar da wani bayani a yau, wanda a cikinsa take jaddada yin tir da Allawadai da kisan babban malamin addinin muslunci Ayatollah Sheikh Baqir Nimr da mahukuntan masarautar iayalan gidan saud a shekarar da ta abata.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarat cwa, Shafin yada labarai na Islamin CC ya bayar da rahoton cewa, jam'iyyar ta Islamic Party wadda daya ce daga manyan jam'iyyun siyasa a kasar Azarbaijan, ta fitar da wannan bayani ne a daidai okacin da ake tunawa da cika shekara guda kisan gillar da masarautar Al Saud ta yi wa Sheikh Nimr ta hanyar sare masa kai, a ranar 2 ga watan Janairun shekarar da ta gabata.

Bayanin ya ce ko shkaka babu, wannan mummunan aiki yana daga cikin abubuwa mafi muni da aka aikata a wannan karini, wadanda tarihi ba zai taba mantawa da su, kamar yadda kuma hakan zai zama wani masomi na kawo karshen mulkin kama karya na 'ya'yan Saud.

Haka nan kuma bayanin ya yi kakkausar suka a kan kasashen da ke da'awar kare hakkin bil adama, wadanda suka yi gum da bakunansu kan wannan mumman aiki da aka tafka, na kisan babban malamin addini saboda dalilai na siyasa da banbancin mazhaba.

Ayatollah Baqir Nimr dai ya kasance mutum mai son ganin an yi adalci a tsakanin al'umma, wanda kuma hakan shi ne babban abin da ya ya jawo fushin masarautar iyalan gidan Saud a kansa, kuma akan haka ne suka fille masa kai.

3559705


captcha