IQNA

19:43 - January 07, 2017
Lambar Labari: 3481110
Bangaren kasa da kasa, tawagar ‘yan majalisar dokokin kasar Iran karkashin jagorancin Alauddini Burujardi ta gana da babban sakataren Hizbullah Sayyid Hassan nasrullah.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakaloto daga shafin tashar Alalam cewa, a yayain ganawar Jakadan Iran a Beirut Muhammad Fath Ali ya kasance a wurin.

Sayyid Hassan Nasrullah, a yayin wannan ganawa ya tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Rahoton ya ce bayan ganawa da Sayyid Nasrullah, tawagar ta gana da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon Nabih Birri, inda a nan ma suka tattauna wasu lamurra da suka shafi abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya musamman ma batun rikin Syria da aka haifar.

Burujardi ya ce mun yi imanin cewa, shugabancin majalisar dokokin kasar Lebanon karkashin nabih Birri ya taimaka matuka wajen warware badakalar matsalar shugabancin kasar, saboda matakai da ya daukia na hikima.

Wanann ziyara dai ta zo ne bayan kammala wani rangadi da tawagar ta yi a kasar Syria, inda a yau suka shiga Lebanon domin ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar suka hada da shugaba Michel Aun.

3560489


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: