IQNA

23:05 - January 09, 2017
Lambar Labari: 3481116
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin muslunci ya fitar da sakon ta’aziyya na rasuwar Sheikh Hashemi Rafsanjani.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci ya fitar da sakon jagoran akan rasuwar Ayatullah Hashimi Rafsanjani.

Matanin sakon kamar haka:

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun.

A cikin bakin ciki da damuwa mu ka sami labarin rasuwar tsohon abokin fafutuka da gwgawarmaya, a zamanin gwagwarmaya da yunkurin musulunci. Abokin aiki ne na kusa da kusa a tsawon lokaci a karkashin jamhuriyar musulunci, wato Hujjatul Islam Wal Muslimin Haji Sheikh Akbar Hashimi Rafsanjani.

Rashin abokin gwagwarmaya kuma abokin tafiya da wanda tarihin tarayyarmu a aiki da abota ya kai shekaru 59 da su ka kasance cikin tsanani da wahala.! Wahalhalun da mu ka shiga tare a cikin wadannan shekarun suna da yawa, kuma abotarmu ta kasance cikin kyakkyawar niyya a wacce ta ci zango-zango daban-daban akan tafarkin da mu ka yi tarayya da shi, cikin tarbar aradu da ka.

Kaifin kwakwalwar da ya ke da ita, da kuma tsarkin niyyarsa mara tamka a tsawon wadannan shekarun, yakasance wanda ake jingina da shi cikin nutsuwa da gaskatawa ga dukkanin wadanda su ka yi aiki da shi, musamman ma dai ni. Banbancin ra'ayi da ijtihadi daban-daban, a cikin tsawon wannan lokacin, bai taba yanke igiyar abotar da ta fara a tsakanin haramai biyu ba ( Imam Husain da Abul Fadal ) a karbala. Kuma kwarmaton masu yawo da zance a tsawon shekarun bayan nan,domin cin moriyar wannan sabanin, bai iya gurbata alaka mai zurfi a tsakanin marigayi da ni ba.

Ya kasance abin koyi mara tamka, na zangon farko na'yan gwagwarmayar da tsarin zalunci na sararuta, kuma yana cikin wadanda aka azabtar akan wannan godaben wanda ya ke cike da hatsari da kuma alfahari. Shekarun zaman kurkuku da dauriyar azabtarwa a hanun Savak, ( jami'an leken asirin Sha) da tsayin daka wajen fuskantar wannan, da aiki mai hatsari a lokacin yakin tsaron kasa mai tsari ( yaki da Iraki) da shugabanicn majalisar shawarar musulunci da majalisar kwararru, da waninsu, suna daga cikin shafuka masu haske na rayuwar wannan tsohon dan gwagwarmayar da ta kasance cike da fadi tashi.

Yanzu da aka yi rashin Hashimi Rafanjani, babu wani mutum da na sani wanda muka yi tarayya da shi akan abubuwa masu yawa na tsawon lokaci, mu ka kuma ga fadi tashi a cikin wannan lokaci na tarihi. Yanzu wannan tsohon dan gwagwarmayar yana a gaban hisabin Ubangiji na ayyukan da su ke cike da fadi tashi, wanda shi ne makomarmu baki daya jami'an jamhuriyar musulunci.

Ina rokongafara da rahamar Allah a gare shi daga cikin zuciyata.Ina kuma yi wa maidakinsa da yayansa da yan'uwansa da danginsa ta'aziyyya.

Sayyid Ali Khamnei.

19/10/1395

3560930


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: