IQNA

23:08 - January 12, 2017
Lambar Labari: 3481128
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da zama dangane da kisan kiyashin da ake yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar Malaysia ya bayyana cewa, a cikin mako mai zuwa ne za a gudanar da zama na ministocin harkokin wajen kasashen musulmi a birnin Kualalampor fadar mulkin kasar Malysia.

Babbar manufar gudanar da wannan zaman taron dai ita ce tattauna yin dubi kan halin da musulmin kasar Myanmar suke ciki, dangane da kisan gillar da sojojin kasar gami da 'yan addinin Buda masu tsatsauran ra'ayi suke yi a kansu.

Zaman dai zai gudana ne a ranar 19 ga wannan wata na Janairu, tare da halartar ministocin harkokin waje na kasashen musulmi 56 mambobi a kungiyar.

Kasar Malaysia dai na daga cikin kasashen yankin gabashin Asia da suka mayar da hankali kan kisan kiyashin da ake yi wa musulmi a Mayanmar, inda a kwanakin baya ta bukaci kungiyar kasashen gabashin Asia da su sak eyin nazari kan matsayin Myanmar a kungiyar, saboda kisan gillar da take yi wa musulmi 'yan kasar.

3561989


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: