IQNA

22:20 - January 14, 2017
Lambar Labari: 3481134
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron kasar Aljeriya sun gano gungun wasu mutane da suka hada da 'yan kasashen ketare da suke yi wa Isra'ila ayyukan leken asiri a kasar, an kuma cafke su baki daya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta Press TV ta nakalto daga shafin jaridar kasar Aljeriya ta Annahar, wadda ta bayar da rahoton cewa an cafke mutanen ne a lardin Garadiyyah da ke yammacin kasar ta Aljeriya, kuma muhimmin aikinsu shi ne haifar da yamutsi da tashin hankali da matsalolin tsaro a kasar.

Dukkanin mutanen sun fito ne daga kasashen Libya, Ethiopia, Ghana, Najeriya, Mali da Kenya, kuma bisa ga tambayoyin da aka yi musu da kuma bayanna da suka bayar, sun tababtar da cewa Isra'ila suke yi wa aiki a kasar ta Aljeriya.

Daga cikin abubuwan da aka samu a wurin da suke zaune, akwai takardu wadanda da ke dauke da rubutun Ibraniyanci (Hebru) harshen da ake magana da shia hukumancea Isra'ila, sai kuma wasu hotuna na bidiyo na zanga-zangar da aka yi kan kyamar gwamnati a kasar a cikin 'yan kwanakin da suka gaba.

Jami'an tsaron na Aljeriya sun tabbatar da sun samu karin wasu abubuwan da suke tabbatar da cewa mutanen suna yi wa Isra'ila aiki ne, da nufin hargitsa kasar ta Aljeriya.

3562413


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، Aljeriya ، Libya ، Ethiopia ، Ghana ، Najeriya ، Mali ، Kenya ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: