IQNA

22:09 - January 16, 2017
Lambar Labari: 3481140
Majiyoyin labarai daga jihar Borno a tarayyar Nigeria sun bayyana cewa wasu boma bomai guda biyu sun tashi a cikin wani masallaci a cikin Jami'an maiduguri a safiyar yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, shafin yada labarai na yanar gizo na saharareporters ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto wata majiya daga birnin Maiduguri yana cewa boma boman guda biyu sun tashi ne a dai dai karfi 6.30 na safe, a cikin masallaci a cikin Jami'an maiduguri inda daliban jami'ar da dalibansu da dama suke bada faralin Asubaha.

Labarin ya kara da cewa har wani yaro dan shekara bakwai ne ya tada boma boman a masallacin JS kusa da gidajen malamai a jami'an kuma yan sanda sun tabbatar da mutuwar Parfesar Aliyu Mani shugaban sashen Vetenary medicine ko kuma lafiyan dabbobi na Jami'an da kuma wasu mutane hudu sannan mutane sha biyar sun ji rauni..

A halin yanzu dai Jami'an tsaro sun killace masallaci don bincike, a yayinsa jami'an agaji na NEMA masu bada taimakon gaggawa suka kwace gawaki da kuma wadanda suka ji rauni zuwa asbiti.

3563228


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: