Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Independent cewa, majalisar musulmin kasar Amurka ta yanke shawara a kan cewa za ta shigar da kara a kan sabon shugaban kasar Donald Trump sakamakon abin da yake yi a kansu na cin zarafi saboda addininsu wanda hakan ya yi hannun riga da dokokin kasar Amurka.
Trump ya sanya hannu kan dokar hana musulmi daga kasashe 7 na musulmi shiga kasar Amurka har tsawon kwanaki 90 da kuma hana izinin shiga kasar na tsawon kwanaki 120 ga yan gudun hijira, daga cikin kasashen da ya hana shiga Amurka kuwa har da na jamhuriyar muslunci ta Iran.
Ya shahara da tsanin kiyya ga musulmi, tun a lokacin yakin neman zabe ya sha alwashin cewa zai hana musulmi shiga Amurka matukar dai ya lashe zabe, wanda kuma abin da yake yia halin yanzu yana a matsayin aiwatar da abin da ya yi alkawali ne.
A ranar Litinin mai zuwa ce dai musulmin kasar ta Amurka za su shigar da kara a hukumance a kan Donald Trump dangane da abin da yake na saba doka kasar kasar.