Bangaren kasa da kasa, Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci hubbaren marigayi Imam Khomeni (RA) da wasu daga cikin shahidan juyin Islama, a daidai lokacin da ake fara bukukuwan zagayowar ranakun fajr na juyin Islama a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta
cewa, Ayatollah Sayyid Ali
Khamenei a yayin ziyarar tasa, ya ziyarci kabrukan wasu daga cikin wadanda suka
bayar da gudunmawa wajen kafa jamhuriyar muslunci,inda ya fara da kabarin
Ayatollah Hashemi Rafsanjani, wanda ya rasua 'yan makonnin da suka
gabata.
Bayan na kuma ya ziyarci kabrukan Shahid
Beheshti, tsohon alkalin alkalan kasar da kuma Rajae tsohon shugaban kasar gami
da Bahonar tsohon firayi ministan kasar, wadanda dukkaninsu suka suka yi
shahada wajen bayar da gudunmawa ga juyin Islama.
Haka nan kuma jagoran ya ziyarci kabrukan
wasu daga cikin wadanda suka yi shahada a wurin akre wurare masu tsarki na
musulmi, da kuma wadanda suka rasa rayukansu daga cikin 'yan kwana-kwana a
cikin makon da ya gabata, a lokacin kashe gobara a ginin Palsco a birnin
Tehran.
3569240