IQNA

19:51 - February 05, 2017
Lambar Labari: 3481201
Bangaren kasa da kasa, kwamitin da ke kula da littafai a Masar ya kore korafin da takfiriyawan salafiyya na kasar ke yi kan cewa akwai littafan mazhabar shi’a a wajen baje kolin littafai na kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, shafin labarai na Arabic.com ya yabar da rahoton cewa, Haisam Alhaj shugaban kwamitin kula da harkokin littafai a kasar Masar ya bayyana cewa, babu wani bayani da suka samu a kan cewa an shigo da littafai da suka sabawa shari’a a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa abirnin Alkahira.

Ya ce dukkanin littafan da aka shigo da su daga wajen kasar kasuwar baje kolin an bincika su kuma an tabbatar da cewa ba su sabawa musulunci ba, saboda korafin da ‘yan salafiyya suka gabatar masa na cewa an kawo littafan shi’a a wurin to shi ba shi da labarin hakan, kuma idan ma har haka ne ai kasar Masar kasa ce wadda ta hada dukkanin bangarori na musulmi wanda kowa yake da ‘yancin bin koyarwar akidarsa da mahangarsa a cikin muslunci.

Shi ma a nas bangaren Ahmad Rasim Annasim wani daya daga cikin masana a kasar ta Masar kuma mabiyin mazhabar shi’a yya bayyana cewa, ‘yan salafiyya duk sun bi sun ruda jama’a da cewa akwai lttafan shi’a a cikin kasuwar baje koli, kuma har yanzu ba su kawo wani littafi guda daya ba da suka gani na shi’a a wurin.

Ya ce lokaci ya wuce da mutum zai ce sai akidarsa ko mahangarsa ce kawai dole kowa zai bi, mutane ba tumaki ba ne, kowa yan ada hankali babu yadda mutum zai yarda da wani abu ba tare da hujja ba, me yasa ake tsoron hjujja ne, mai mai tsoron hujja sai maras huja.

3570690


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: