IQNA

22:30 - February 13, 2017
Lambar Labari: 3481228
Bnagaren kasa da kasa, babban dakin adana kayan tarihi na birnin New York na shirin nuna wasu dadaddun hotunan musulmi da suka rayu a birnin.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Gothamist cewa, za a gudanar da wannan baje kolin hotunan musulmin ne domin mayar da martani da umarnin Donald Trump na hana wasu musulmi shiga cikin kasar Amurka.

Daga cikin hotunan da za a nuna kuwa har da wadanda suke komawa zuwa ga shekaru na 1940, da ke yadda musulmi suka kasance a lokacin da kuma rayuwarsu a cikin New York na Amurka da yadda suke rayuwa lai lafiya tare da kowa ba tare da wata matsala ba.

A cikin shekarun 1960 ne aka samu wasu canje-canje a cikin dokokin hijira da shigar baki a kasar ta Amurka, bayan nan kuma an kara samun karuwar yawan musulmi da suke rayuwa a cikin birnin New York, inda a halin yanzu fiye da musulmi dubu 300 ne ke rayuwa acikin birnin.

Babban darakta dakin adana kayan tarihi na birnin bayyana cewa, za su nuna wadannan hotuna ne domin su tabbatarwa al’ummar Amurka cewa musulmi ba baki ba ne a birnin New York, domin kuwa musulmi sun fara rayuwa a New tun kimanin shekaru dari uku da suka gabata.

Ya kara da cewa birnin New York birni ne da ya kunshi mutane masu al’adu daban-daban da kuma addinai daban-daban, wannan kuma babban ci gaba da birnin ya samu shi yasa hakan ya zama abin alfahari gare su.

Za A Nuna Tsoffin Hotunan Musulmi A Dakin Kayan tarihi Na Birnin New York

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: