IQNA

An Fitar Da Littafi Mai Taken (Sulhu Da Yaki A Kur’ani) A Karbala

21:44 - February 17, 2017
Lambar Labari: 3481237
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke kula da hubbaren Imam Husain a Karbala ta fitar da wani littafi mai taken sulhu da yaki a cikin kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga cibiyar kula da hubbaren Imam Hussain (AS) a karbala cewa, Ala Almaliki daya cikin marubuta kuma masu bincike a ilmomin kur’ani ya rubuta littafin mai taken sulhu da yaki a cikin kur’ani mai tsarki, wanda wannan cibiya ta dauki nauyin bugawa.

Baynin ya ci gaba da cewa wannan marbci wanda ya shahara a kasar Iraki ta fuskar rubuce-rubuce musamman a bangaren kur’ani, ya rubuta wannan littafi ne a cikin shafuka 300 da babobi 5, inda ya yi bayani dalla-dalla kan ma’anar wadannan kalomi a cikin littafi mai tsarki.

A babi na farko ya yi bayani ne kan ma’anar kalmomin sulhu da kuma yaki a cikin kur’ani mai tsarki, kafin daga bisania cikin sauran babobin ya fadad abayani na ilimi da bincike a kansu, tare da bayyana mahangar kur’ani a kan dukkanin kalmomin biyu.

Musulunci dai addini ne wanda akowane lokaci yak an fifit sulhu da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakaninsa da sauran al’ummomi, kuma yaki yakan zi ne a matsayin kariyar kai daga makiya da suke afkawa musulmi ko kuma suke yin barazana a kan musulmi.

3575274


captcha