Hukumar agaji da samar da ayyukan yi ga ‘yan gudun hijira ta Falasdinu UNRWA ta sanar a jiya Asabar cewa sama da malamai 8,000 a shirye suke da su taimaka wa yara kanana su koma karatu da kuma ci gaba da ayyukan makaranta a zirin Gaza.
Hukumar UNRWA ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa ita ce kungiyar agaji mafi girma a Gaza kuma ya kamata a bar ta ta gudanar da ayyukanta ba tare da tsangwama ba.
UNRWA ta lura cewa yara a Gaza ba su iya zuwa makaranta na dogon lokaci.
Yakin da yahudawan sahyoniya suka yi a Gaza ya yi sanadiyar shahadar mutane kusan 68,000. Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa sun lalata ababen more rayuwa da galibin makarantun, kuma dalibai sun kasa zuwa makaranta kusan shekaru biyu.