IQNA

20:49 - February 18, 2017
Lambar Labari: 3481240
Bangaren kasa da kasa, wani mutum mai fasahar zane-zane a kasar Masar ya fitar da wani zane da ke dauke da ayar kur'ani mai tsarki domin fadakarwa.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, shafin jaridar yaum Sabi ya habarta cewa, Farid Amara wani masanin ayyukan zanen fasaha ne a kasar Masar, ya kuma yi zane da ke dauke da ayar kur'ani mai tsarki da ke fadakar da 'yan adam a kan kusancin kiyama a rayuwarsu, wanda kuma ya samu karbuwa a shafukan yada zumunta musammna Facebook.

Wannan zane dai ya nuna yadda wannan aya ta yi daidai da yanayin rayuwar jama'a ta wannan zamani, kuma an fitar da shi ne tun a cikin shekara ta 2012, wanda ke nuna wani batiri da yake aiki kuma karfinsa yana tafiya har ya kusa karewa.

Duk kuwa da cewa wannan aya ta safka tun fiye da shekaru dubu da dari hudu da suka gabata, amma Allah madaukakin sarki yana tunatar da dan adam kan cewa hisabin mutane ya kusa wato kiyamarsu ta karato tana gab da tashi, amma kuma suna cikin dimuwa da mantawa da Allah da kuma tashin kiyama.

A kowane lokaci tunatarwa gad an adam mai Imani tana da na amfani, a akn haka wannan mutum ya himmatu matuka wajen yin amfani da irin fasahar da Allah ya bashi domin yin fadakarwa da kuma tunatar da mutane lahira da hisabi da ke jiransu a kan dukkanin abin da suka aikata a rayuwar duniya.

Amarah ya yi amfani da hkima matuka wajen zabar kalolin da ya yi zanen da su, ta yadda za su bayar da tasirin da yake bukata a cikin zuciyar duk wanda ya kalli zanen.

3575410


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: