IQNA

23:27 - February 19, 2017
Lambar Labari: 3481244
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasuwar baje kolin littafai da ake gudanarwa a Morocco ya bayyana cewa kur’ani shi ne littafin da aka fi saye a wannan baje koli.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin hespress cewa, Fu’ad babban daraktan kasuwar baje kolin littafai da ake gudanarwa a birnin kazablanka na kasar Morocco ya bayyana m kwafin kur’ani shi ne aka fi saye afadin baje kolin.

Ya ci gaba da cewa wannan baje koli na duniya yana daga cikin irinsa da aka saba gudanarwa a kasar fiye da shekaru ashirin da suka gabata, amma a shekarar bana abin ban mamaki shi ne yadda masu halartar wurin suka mayar da hankali ga kur’ani matuka.

Dangane da yanayin cinikin littafan kuwa, Fu’ad ya bayyana cewa bana cinikin ya yi kasa matuka, wanda hakan kuma ya sanya madaba’antu da ke buga littafai cikin damuwa, musamman ganin cewa sun fitar da kudade domin buga littafai masu tarin yawa, amma kuma babu ciniki sosai kamar shekarun baya.

Kasuwar baje kolin dai tana gudana ne abirnin kazablanka daya daga cikin manyan biranan kasar Morocco, inda aka baje littafai da aka rubuta abangarori daban-daban na ilimi.

A yau ne za a kammala gudanar da wannan kasuwa baje kolin littafai ta duniya, da ake gudanarwa akasar Moro a karo na 23 tare da halartar madaba’antu daga kasashe 54 na duniya.

3575870


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: