IQNA

23:43 - February 25, 2017
Lambar Labari: 3481262
Bangaren kasa da kasa, Asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya amince da wasu daga cikin shawarwarin da bankin musulunci ya gabatar dangane da harkokin kudade a bankuna.


Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarat cewa, Shafin yada labarai na Al-bilad ya bayar da rahoton cewa, Asusun IMF ya bayyana hakan ne bayan yin nazari a kan wasu daga cikin shawarwari da bankin muslunci ya gabatar, kan wasu batutuwa da suka shafi hada-hadar kudade a bankuna.

Bayanin ya ce bankin muslunci yana da nasa tsare-tsaren da suka ginu a kan tsarin kudi a mahanga ta muslunci, wadanda ake tafiyar da su ta hanyoyi na zamani, da hakan ya hada da ajiyar kudi ba tare da karbar riba ba, da kuma saka hannayen jari da tsarin raba ribar da bankin ya samu a tsakanin masu hannun jari, da dai sauran tsare-tsare makamantan hakan.

Tun a cikin shekaru 90 bankin muslunci yana da kudade da kaddarori suka kai na dala biliyan 100, amma a cikin shekarar da ta gabata, bankin ya sanar da cewa kudade da kaddarorinsa sun kai na dala trilion 1.5 kuma kimanin kasashe 60 suke da kudade da kaddarori a cikin bankin, da suka hada da na gabas ta tsakiya da kuma Asia.

3577861


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: