IQNA

Taron TunawaDa Shahadar Fatima (AS) A Philipines

23:25 - March 02, 2017
Lambar Labari: 3481278
Bangaren kasa da kasa, a daren yau za agudanar da zaman taro na tunawa da shahadar Fatima Zahra (AS) a kasar Philipines.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin manila na kasar Philipines ya sheda cewa, a yau za a gudanar da taron du’aul Kumail.

Bayan kammala taron addu’ar kuma za ashiga taron tunawa da shahadar Sayyid Zahra (SA) inda Iraniyawa mazauna birnin gami da mabiya tafarkin iylan gidan manzo da ma sauran musulmi da suke da sha’awar halarta za su taru.

Karamin ofishin jakadancin Iran ne zai dauki nauyin shirya wannan zaman taron kamar yadda aka saba yi a duk lokacin gudanar da wani taron tunawa da hahihuwa ko shahadar daya daga cikin limaman ahlul bait da iyalan gidan manzo.

Malam Mujtaba Akbari shugaban jami’ar Almostafa birrnin Manila ne zai gabatar da jawabi a wurin.

3580007


captcha