IQNA

Tawagar Masu Kai Dauki Ga Musulmin Myanmar Daga Aljeriya

23:40 - March 03, 2017
Lambar Labari: 3481280
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar masu kai dauki daga kasar Aljeriya na shirin kama hanya zuwa kasar Myanmar domin kai kayan taimakon ga musulmin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Bu Shaibah shi ne shugaban tawagar masu kai agaji da dauki zuwa ga musulmin Myanmar.

Ya bayyana cewa sun kammala dukkanin shirinsu domin tafiya Myanmar da nufin kai kayan agaji da taimako ga msuulmin kasar wadanda ake yi wa kisan kiyashi daga jami'an gwamnatin kasar da kuma masu tsananin akidar addinin buda.

Dangane da lokacin tafiyar tasu ya bayyana cewa nan da 'yan kawanaki kadan masu zuwa a karkashin cibiyar Irshad wa Islah za su tafi zuwa Turkiya, daga can kuma za su kama hanya zuwa Myanmar, inda za su hadu da musulmi da kuma basu kayayyakin taimako da wannan cibiya ta tanada, da suka hada da abinci da magunguna da sauran abubuwan bukatar rayuwa.

Ya ce halin da musulmin kasar Myanmar suke ciki ya yi muni matuka, kuma wajibi ne a kan dukkanin msuumi a duk inda yake ya kai dauki ga wadannan bayin Allah da suke cikin kunci na rayuwa.

Gwamnatin Myanmar dai ta kare kanta dangane da kisan kiyashin da take yi wa musulmi marassa rinjaye a kasar da cewa, ana kare dokar kasa ne, kuma abbu gaskiya a kan rahotannin da ake bazawa na kisan kare dangi a kan musulmi 'yan kabilar Rohingya.

3580138

captcha