IQNA

Musulmi Dan Takarar Gwamnan Jahar Michigan Ta Amurka

23:45 - March 03, 2017
Lambar Labari: 3481281
Bangaren kasa da kasa, a karon farko wani musulmi ya fito a matsayin dan takarar neman gwamnan jahar Michigan ta kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, Abdulrahman Muhammad sayyid wani wanda likita ne musulmi dan asalin kasar masar, ya bayyana aniyars ta tsayawa takarar neman kujerar gwamnan jahar Michigan ta kasar Amurka.

Ya bayyana cewa yana fatan samun nasara a wannan zabe da za a gudanar na zaben jahohi da kuma kananan hukumomi a kasar Amurka, inda ya bayyana cewa zai girmama dukkanin akidu da addinai na al'ummar Amurka matukar dai ya lashe zabe, domin kuwa a cewarsa addini da akida suna da matukar muhimamnci a wurnsa, saboda haka dole ne shi ma ya girmama addini da akidar wasu.

Idan har Abdulrahman Muhammad Sayyid dan shekaru 32 da haihuwa ya samu nasarar lashe zaben, zai zama shi ne gwamna musulmi na farko a kasar Amurka, haka nan kuma zai zama shi ne gwamna na farko a tarihin kasar mafi karancin shekaru.

Jahar Michigan dai na daga cikin jahohin da aka fara samun karuwar kymar musulmia cikin lokutan nan, amma kuma ga dukaknin alamu Muhammad sayyid yana da farin inin da zai iya lashe zaben gwamnan jahar a zagayen farko.

3580149

captcha