IQNA

22:03 - March 04, 2017
Lambar Labari: 3481283
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasare Mauritania domin fitar da wadanda za su wakilci kasar a gasar kur’ani ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Sahra Media cewa, an fara gudanar da wannan gasa ne a babban masallacin madinatul Munawwarah da ke birnin Nuwakshout fadar mulkin kasar.

Ana gudanar da gasar ne a bangarorin harda, karatu kuma tafsirin kur’ani mai tsarki, kamar yadda kuma dukkanin bangarorin ana la’akari da sanin iliminhukunce-hukuncen karatu wato tajwidi.

Ma’aikatar kula da harkokin ilimin addinin muslunci ta kasar Mauritania ce ke jagorantar gudanar da wannan gasa, inda kuma a nan ake fitar da wadanda za su wakilci kasar a sauran tarukan gasar kur’ani na kasa da kasa a cikin wannan shekara.

Mutane 214 ne suke halartar gasar da suka hada da maza d akuma mata, 48 daga cikinsu a bangaren tafsirin kur’ani mai tsarki, 28 daga cikinsu kuma a bangaren sanin ilimin hukunce-hukuncen karatun kur’ani mai tsarki.

Ahmad Wuld Dawud ministan ma’aikatar kula da harkokin ilimin addinin muslunci na kasar Mauritania ya bayyana a gaban taron bude gasar cewa, babbar manufar wannan gasa kamar yadda aka saba yi kowace shekara itce tantance wadanda suka fi nuna kwazo domin su wakilci kasar a sauran gasar da za a gudanar a mataki na duniya a cikin wannan shekara.

Ya kara da cewa, gudanar da gasar kur’ani wata dama ta wayar da kan matasa dangane da abun da ya shafi kur’ani, kamar yadda kuma ta hakan za a iya yi masu saiti, maimakon bin son ran wasu da suke wasa da hankulan matasa yadda suka ga dama, kuma har su yi amfani da su domin ayyukan ta’addanci.

3580241

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Mauritania ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: