Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa an fara aiwatar da wani shiri mai taken kur'ani ne rayuwata akasar Jordan, wanda gidan radiyon hayat tare da hadin gwaiwa da bankin Dubai suke gudanarwa.
Babban abin da wannan shiri yake mayar da hankali a kansa shi ne kokarin jawo hankalin matasa zuwa ga koyarwar kur'ani, musamman a wannan lokaci da ake kokarin gurbata al'adun musulmi zuwa al'adun turawan yamma.
Da dama daga cikin masu bin wananns hiri sun nuna gamsuwarsu matuka dangane da yadda shirin yake gudana, musamman ganin cewa ana gayyatar malamai masana da suke gabatar da jawabai da bayanai kan manufofin ayoyin kur'ani, da kuma yadda musulmi zai yi aiki da su a rayuwarsa ta zamantakewa.
Bankin Dubai dai an samar da shit un a shekara ta 2010, kuma wadannan na daga cikin ayyukan da yake gudanarwa na kara yada addinin muslunci da koyarwarsa a cikin al'umma.
3581570