IQNA

Cibiyar Musulmin Amurka Ba Ta Amince Da Sabuwar Dokar Trump Ba

23:41 - March 08, 2017
Lambar Labari: 3481296
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar msuulmin kasar Amurka ba ta amince da sabuwar dokar Donald Trump ta nuna kyama ga musulmi ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Islamic News cewa, Nahad Iwad babban sakataren cibiyar msuulmin Amurka ya bayyana cewa, matakin da Donald Trump ya dauka na nuna kyama ga musulmi ya sabawa abin da ke rubuce a cikin kundin tsarin mulkin Amurka.

Ya ce cire kasar Iraki daga cikin jerin sunayen kasashe 7 da Trump ya haramta ma shiga Amurka wata ‘yar karamar nasara ce, amma duk da haka har yanzu akwai ksashen musulmi 6 da Trump ya haramta musu shiga Amurka.

Nahad ya ce ba za su zura ido sunan kallon lamarin yana ci gaba da tafiya a haka ba, ana nuna mus wariya da kyama a hukumance, za su ci gaba da bin matakan da suka dace domin kalubalantar wannan lamari, da hakan ya hada har da bin matakai na shari’a.

Tun lokacin da Dolad Trump ya dare kan kujerar shugabancin kasar Amurka ya fara daukar matakai na nuna tsananin kyama ga musulmi, inda bai yi wata-wata ba wajen kafa dokar hana wasu kasashe bakwai shiga cikin Amurka, inda ya bayyana cewa mutanen wadannan kasashe suna a matsayin barazana ne ga Aurka ta fuskar tsaro, sakamakon yawaitar ayyukan ta’addanci da ake fama da su.

Sai dai kuma hukumomin tsaro na kasar ta Amurka sun tabbatar da cewa, babu ko daya daga cikin mutanen kasashen da Trump ya ayyana a matsayin barazana ga Amurka, da ya taba kai wani harin ta’addanci a kasar.

3582005

captcha