IQNA

Wani Masani Dan Najeriya:

Sahihiyar Fahimtar Kur'ani Tana warware Matsalolin Al'umma

20:38 - March 11, 2017
Lambar Labari: 3481304
Bangaren kasa da kasa, wani masania tarayyar Najeriya ya bayyana cewa, sau tari matsalolin da al'umma ke fuskanta na da alaka ne da rashin sanin koyarwar kur'ani a kan lamarin rayuwarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Guardian cewa, Imam Yunus wani masani ne kan harkokin addini a Najeriya, ya bayyana cewa cewa babban abin da ke a gaban musulmi shi ne su fahimci hakikanin koyarwar kur'ani mai tsarki, a lokacin za su samu waraka a kan matsalolinsu na zamantakewa da sauransu.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatr da wani jawabi a birnin Lagos babbar cibiyar kasuwanci ta Najeriya, inda ya bayyana cewa cibiyarsa ta mayar da hankali wajen koyar da musulmi larabci, domin su iya karanta kur'ani da hadisan manzo (SAW) su fahimce da kyau.

Ya ci gaba da cewa yana da matukar muhimmanci ga musulmi a duk inda yake ya fahimce abin da kur'ani mai tsarki ke koyar da shi, kuma ya san addini ta hanyar koyarwar ma'aiki wanda shi ne babban malamin kur'ani mai bayyana ma'anoninsa ga talikai.

Daga karshe ya kira kirayi musulmi da ma wadanda ba msuulmi da su san cewa a kowane lokaci shi addinin muslunci yana kira ne zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsa da sauran addinai, musulunci ba addinain tashin hankali ba ne, addini ne na girmama dan adam da mahangarsa da kuma fahimtarsa.

3582822
captcha