Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jaridar Telegraph ta bayar da rahoton cewa, jam’iyyar firayi ministan kasar Holland Mark Rutte ta sake lashe zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.
Shugaban hukumar zaben kasar Holland Tamara Ven ya bayyana cewa, dukkanin bangarorin sun taka rawar da ya kamata a wannan zabe, kuma ba a samu wata matsala ba, duk da cewa dai har yanzu jam’iyyar Firayi ministan kasar ita ce tafi sauran jam’iyyu yawan kujeru da ta lashe na majalisar dokokin kasar.
Sai dai a nasa bangaren Geert Wilders fitaccen mutumin da ke gaba da addinin muslunci a kasar ya sha kashi inda jam’iyyarsa ta kasa tabuka abin a zo gani, domin kuwa jam’iyyar frime ministan kasar ta yi mata fintikau.
Kafin wannan lokacin dai Geert Wilders ya bayyana wuraren yakin neman zabe kan cewa, idan har jam’iyyar ta lashe zaben majalisa, to zai kafa dokokin da za su haramta gina masallatai da kuma cibiyoyin addini.
Bayan sanar da cewa jam’iyyar ta sha kashi ya bayyana cewa hakan ba zai hana shi gaba da kamfensa na nuna kiyya da muslunci ba a cikin kasarsa da ma sauran kasashen turai.