IQNA

An Bata Hukuncin Daurin Shekaru 9 A Kan Sheikh Ali Salman

23:14 - April 03, 2017
Lambar Labari: 3481371
Bangaren kasa da kasa, Kotun karya shari'a a Bahrain ta sassauta da shekaru biyar hukuncin zama gidan yari ga jagoran 'yan adawa na kasar dan shi'a nan Sheikh Ali Salman.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, kotun masarautar mulkin kama karya ta sassauta hukuncin daurin shekaru 9 da ta yanke a kan sheikh Ali Salamn jagoran adawar siyasa da neman canji na dimokradiyya a kasar zuwa shekaru hudu.

A shekera 2015 ne wata kotu a kasarta yankewa Sheikh Ali hukuncinzamen gidan kasona shekara biyar, aman daga bisani kotun daukaka kara ta tsawaita masa hukuncinzuwa shekara tara a shekara 2016 data gabata.

Sheikh Ali Salman, dan shekaru 51 ana daimasarautar Bahrain tana zarginsa da tada fitinada kuma kin biyaya ga wasu dokoki da suka rataya ga dankasa, wanda dukkanin zarge-zargen suke da alaka da siyasa da kuma banbancin mazhaba.

DaureSheikh Ali da kuma soke kungiyarsa ta Al-Wefaq dakotu ta yi a shekara 2014 ya janyo zanga-zanga ba kadan ba a wannan kasa ta Bahrainda kuma Allah wadai na wasu kasashen duniya da suka hada da Amurka da Iran da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.

3586476

captcha