IQNA

Musulmin Kenya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Yunkurin Rusa Masallaci

23:36 - April 08, 2017
Lambar Labari: 3481387
Bangaren kasa da kasa, dubban musulmi a birnin Nairobi na kasar Kenya sun gudanar da jerin gwano domin nuna rashin amincewa da wani shirin gwamnati na rusa wani masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, musulmin sun gudanar da wannan jerin gwanona kan babban titin da wannan masalalci yake, tare da yin zaman dirshan.

Salim Muhammad shi ne limamain wannan masalalci, ya kuma bayyana cewa yunkurin mahkuntan kasar na rusa wannan masallaci yana tatatre da babbar matsala, domin kuwa dubban muslmi ne suke gudanar da harkokinsu na ibada a wannan wuri.

Ya ce wannan masalalci bai takaitu da salla ba, domin kuwa akwaio makaranta a wurin da ake koyar da yara, kuma gwamnati ba a shirye take ta bayar da wani wuri domin gina wani masalalcin makamancinsa ba.

Haka na kuma ya yi ishara da cewa, bas u da matsala da shirin gina hanya da gwamnati ta ce za ta yi, amma ta biya diyya ga mutanen da abin zai shafa, haka nan kuma ta dauki nauyin bayar da wani wurin da kuma gina wani masalalcin na daban.

Musulmin Kenya dai adadinsu ya kai kashi 11.5 cikin mutane miliyan 46 na kasar.

3587594


captcha