IQNA

Taro A Jami’ar Califirnia Kan Kyamar Musulunci

23:35 - April 17, 2017
Lambar Labari: 3481414
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taro a jami’ar California da aka fi sani da jami’ar Brukly a kasar Amurka kan karuwar kyamar muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aboutislam.net cewa, za a gudanr da wannan taro mai taken kyamar musulmi na nufin kawo karshen akidar librism ne?

An shirya fara gudanar da wannan taron ne dai a ranar Juma’a mai zuwa a dakin taruka na Zaituna da ke cikin wannan jami’a.

Taron dai zai samu halrtar masana da kuma malaman jami’a da dalibai musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, domin yin bahasi kan kyamar musulmi da kuma abubuwan da suke jawo haka, musamman a halin yanzu a kasar Amurka.

Bayanin ya ci gaba da cewa, tuin bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta karbi ragamar iko, kyamar muslmi ya karu matuka a kasar, wanda hakan ke nuni da cewa an saki hanyar rashin nuna banbancin addini wanda kasar ta ginua kansa, kuma yake a rubuce a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Wasu daga cikin ‘yan siyasa a Amurka da suka hada da sabon shugaban kasar, suna amfani da kiyayya ga addinin muslunci saboda cimma manufofi na siyasa da kuma jari hujja, duk kuwa da cewa wasu suna bin wannan akida ta kyamar musulmi saboda rashin sanin musluncin ne.

3590350


captcha