Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Crux Now cewa, dakin cin abinci na Halal a Nairobi na daga cikin muhimman wurare da mabiya addinin kirista suke zuwa domin cin abinci a kasar Kenya.
Kasar Kenya wadda adadin mutanenta kasha 82 cikin dari mabiya addinin kirista ne, amma kuma kuma a lokaci guda musulmi suna gudanar da harkokinsu a cikin ‘yanci musamman ta fuskanci abincin halal.
Adadin musulmi a kasar ta Kenya dai bai wuce miliyan 4 daga cikin mutane miliyan 42 na kasar ba.
Mabiya addinin kirista suna cin abinci a wuraren da musulmi suke sayar da abincinsu na halal, inda suke bayyana cewa abincin musulmi yana da tsafka kuma ana kula da shi ta fuskar lafiya yadda ya kamata.
Tun kafin wannan lokacin da mahukuntan kasar Kenya sun sanya hannu tare da kamfanonin abincin halal daga kasashen musulmi da nufin kara yawan abincin halal da ake samarwa a kasar, saboda musulmi ‘yan yawan shakatawa da suke bukatarsa.
Abdullah Khair wani malami ne a jami’ar Mobasa ya bayyana cewa, wuraren da musulmi suke sayar da abinci ba a samun naman alade ko jaki ko kuma naman kare,kuma ana yanka dabba har sai jininta zuba duka kafin a ci saka namata a abinci.