Kamfanin dukkancin labaran iqna ya habarta cewa, mahukuntan kasar Bahrain sun bayyana ranar gobe Lahadi a matsayin rana ta karshe da za a gudanar da zaman a karshe, inda za a yanke hukunci a kan Ayatollah Sheikh Isa Kasim, babban malamin mabiya mazhabar shi'a na kasar, wadanda kuma su ne fiye da kashi 80 cikin dari na al'ummar kasar Bahrain baki daya.
Bisa ga wasu bayanai da suke fitowa daga majiyoyi na kusa da mahukuntan kasar ta Bahrain, a zaman da kotun masarautar kasar za ta gudanar a gobe Lahadi, za ta yanke hukuncin dauri a gidan kaso a kan babban malamin, da kuma kora daga kasar.
A ranar ashirin ga watan Yunin shekara ta dubu biyu da sha shida, da ta gabata ce masarautar Bahrain ta sanar da cewa ta janye izinin zama dan kasa daga kan malamin dan kasa na asali a Bahrain, bisa tuhumarsa da mara baya ga masu adawa ta tsarin mulkin mulukiya na masarautar kasar, da kuma zargin cewa yana karbar kudaden zakka da khumusi daga mabiyansa ba tare da izinin masarautar ba.
Tun bayan sanar da hakan, jami'an tsaron masarautar Bahrain wadanda akasarinsu ba 'yan asalin kasar ne ba, suna a matsayin ma'aikatan haya ne da aka dauko daga kasashen Pakistan, Jordan da wasu kasashen larabawa, sun yi ta yunkurin kai farmaki a kan gidan babban malamin da ke unguwar Duraz a kusa da birnin Manama, amma hakan ta faskara, sakamakon zaman dirshan da dubban mutane suke yi a kofar gidan nasa tun daga ranar da aka bayar da wannan sanarwa.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, da suka hada da Amnesty Int. Human Rights Watch da sauransu, sun yi Allawadai da wannan mataki na siyasa tsantsa da mahukuntan Bahrain suka dauka a kan babban malami mafi tasiri a fadin kasar, tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin mafi yawan al'ummar kasar ne, tare da kiran sarakunan kasar da su sake yin nazari kan wannan babban kure da suka tafka.