Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto shafin Mir’at Bahrain cewa, kotu ta 4 a Bahrain ta sanar da dage shari’ar Ayatollah Isa Qasem zuwa ranar 21 ga watan Mayu da muke ciki.
A jiya ne dai wannan kotu da ke karkashin umarnin masarautar Bahrain ta sanar da cewa za ta yanke hukunci na krashe akan babban malamin, wanda a kan haka kuma aka dauki matakan tsaro a fadin kasar domin urkushe jama’a.
Kungoyin kare hakkin bil adama na duniya sun kirayi mahukuntan na Bahrain da su gaggauta janye wannan batu na siyasa a kan babban malamin kasar, domin gudun abin da iya kai ya dawo, sai dai ga dukkanin alamu masarautar Bahrain ba a shirye take ta saurari kiraye-kirayen da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya da manyan cibiyoyi masu zaman kansu gami da kungiyoyin addini a duniya suke yi musu ba a kan wannan lamari.
Hakan kuwa sakamakon goyon bayan da take samu kai tsaye daga manyan kasashen duniya, wadanda su ne suke bata kariya kai tsaye tare da sauran 'yan koransu daga cikin kasashen larabawa na yankin gabas ta tsakiya.
Yanzu haka rahotanni suna tabbatar da cewa, tun daga ranar Alhamis da ta gabata ya zuwa daren jiya daruruwan motocin soji masu sulke dauke da dubban sojoji daga kasar Saudiyya, sun shiga cikin kasar ta Bahrain, kamar yadda gidajen talabijin da dama suka nuna hotunansu a lokacin da suke wucewa a kan babbar gadar sarki fahad, wadda ta hada kasashen biyu, wanda hakan ke nuni da cewa za a yi amfani da karfin a kan jama'a wadanda tabbas za su yi gagarumin bore a kasar, matukar aka yanke wani hukunci a kan babban malamin addini na kasar.