IQNA

Taro Mai Take Matsayin Ahlul bait (AS) A Muslunci

23:33 - May 08, 2017
Lambar Labari: 3481493
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken ahlul bait (AS) da matsayinsu a cikin addinin muslunci a kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal ya sanar da cewa, ofishin ne tare da hadin gwiwa da kungiyar darikar Tijjaniya za su gudanar da wannan taro.

Bangaren kungiyar darika na sheikh Abdullah Gey ne zai jagoranci ragamar gabatar da wanann taro, wanda karamin ofishin jakadancin Iran zai dauki nauyinsa, inda za a gabatar da bayanai kan matsayin ahlul bait (AS) a cikin muslunci.

A gefen taron kuma za a gudanar da wani baje koli na kayyakin hubbaren Radawi, da suka hada da hotunan wanann hubbare mai albarka, kamar yadda kuma za a nuan wani fim na musamamn a kan al'adun na addini.

3597237
captcha