Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Jordan cewa, an fara gudanar da wannan zaman tataunawa ne tare da halartar wakilai daga kasashe daban-daban, kuma za a ci gaba da taron har zuwa ranar Alhamis mai zuwa.
Wannan dais hi ne karo na biyu da ake gudanar da wannan zaman taro a mataki na kasa da kasa, wanda yake mayar da hankalia kan batun zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai na duniya.
Muhammad Al’alawi shi ne wakilin ma’aikatar al’adu ta kasar Morocco wanda ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya bayyana cewa kusanto da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai lamari ne mai matukar muhimmanci, musamman a wannan zamani.
Inda ya ce har kulum fahimta a tsakanin al’ummomi da kuma mabanbantan al’adu da addinai na taka gagarumar rawa wajen kyautata zamantakewar jama’a a koina cikin fadin duniya, a kan ya zama wajibi a karfafa irin wannan taro domin samun zaman lafiya da fahimtar juna mai dorewa a duniya.
Muhammad Alalawi ya kara da cewa, wannan taro zai hada bangarori daban-daban, bayan jawabai da kuma laccoci, za a gudanar da wasu abubuwan da suka hada da baje koli da kuma nuna fina-finai.