Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ammar Khuza’i shugaban bangaren hulda da jama’a na cibiyar darul kur’ani ta hubbaren Imam Hussain (AS) ya bayyana cewa, an shirya wannan zama ne a yankunan Aalas da Ajil da ke arewa maso gabashin lardin saluddin.
Ya ci gaba da cewa, babbar manufar shirya wannan zama na karatun kur’ani a wannan rana mai albarka shi ne, kara karfafa muminai da ruhin kur’ani mai tsarki a fagen dagaa wannan rana mai albarka da mabiya ahlul bait (AS) ke raya ta da ayyukan ibada.
Sheikh Husam Sa;idi shugaban bangaren kula da ayyuka na wayar da kai da wa’azi a cikin dakarun sa kai na Hashd Sha’abi ya bayyana a wurin zaman cewa, ko shakka bab cibiyar darul kur’an da ke karkashin hubbaren Imam Hussain (AS) tana bayar da gagarumar gudunmawa wajen karafafa gwiwar mujahidai masu yaki da ‘yan ta’adda.