IQNA

An Bude Cibiyar Koyar Ilmomin Kur’ani Da Hadisi Mai Zurfi A Najaf

23:44 - May 13, 2017
Lambar Labari: 3481509
]Bangaren kasa da kasa, an bude cibiyar koyar ilimin kur’ani da hadisi mai zurfi a birnin najaf na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an bude cibiyar koyar da ilmomin kur’ani da hadisi mai zurfi a karkashin kulawar cibiyar kur’ani da ke karkashin hubbaren Imam Hussain (AS) a birnin Najaf mai alfarma.

Bayanin ya ce wannan cibiya za ta mayar da hankali ne wajen koyar da imomin kur’ani da hadsi mai zurfi domin samar da malamai masu kwarewa mai zurfi a wannan bangare.

Hojjatol Islam Hasam Mansuri shugaban cibiyar kur’ani ta hubbaren Imam Hussain (AS) ya gabatar da jawabia wurin, inda ya jaddada muhimamncin yada ilmomin kur’ani mai tsarki da kuma hadisan amnzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a cikin al’ummar msulmi.

Shi ma a nasa bangaren Allah Sayyid Muhammad Ali Alhulwu ya halarci wrin ya kuma sanya albarka ga wannan cibiya da ayyukanta da ta sanya a gaba.

Kimanin dalibai ‘yan kasar waje 27 gami da wasu daliban kasar Iraki suka fara karatu a wannan cibiya.

3598777


captcha