IQNA

An Bude Talabijin ta Muslunci A Malawi A Farkon Ramadan

23:48 - May 27, 2017
Lambar Labari: 3481556
Bangaren kasa da kasa, an bude talabijin ta muslunci ta farko a kasar Malawi a daidai lokacin da ake fara azumin watan Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin WB cewa, an bude wannan tasha ne mai suna TV Islam, da nufin gudanar da shirye-shirye da ska danganci addinin muslunci da yada zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin musulmi da sauran addinai.

A lokutan baya musulmin kasar Malawi suna kallon tashoshin muslunci, amma ba nasu ne na cikin gida ba, saboda haka abubuwa da dama da suke bukatar sani da suka shafe su da yanayin zamantakewarsu na yi musu wahala matuka ta hanyoyin tashoshin talabijin, ganin su ne kashi 30 cikin kamutane miliyan 17 na kasar.

Jadun Montali shi ne ministan yada labarai na kasar ta Malawi, ya halarci taron kaddamar da wannan gidan talabijin a jiya, inda ya bayyana jin dadinsa matuka dangane da hakan, yana mai cewa haki yay i farin cikin bude wanan tasha, wadda za ta kara taimakawa wajen yada zaman lafiya da fahimtar juna a kasarsa.

Ya ce: ya yi imanin cewa ko shakka babu wannan tashar talabijin za ta taimaka matuka.

3603412


captcha