IQNA

Wata Majami’a Ta Shirya Wa Musulmi Buda Baki A Afirka ta Kudu

23:46 - June 12, 2017
Lambar Labari: 3481605
Bangaren kasa da kasa, wata majami’ar yahudawa ta shiryawa musulmi taron buda baki a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na TRT World cewa, an shirya gudanar da wannan buda baki ne a jiya tare da halartar mabiya addinin muslunci da kuma yahudawa.

Taj Hagi shi ne limamin musulmi a birnin, ya bayyana cewa hakika wannan babban ci gaba ne wanda zai bayar da damar kara bunkasa tattaunawa atsakanin addinai domin kara samun zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsu.

Gorg Alexender shi ne babban malamin majami’ar yahudawan ta Cape Toen ya bayyana cewa, sun shirya wannan taron buda baki ne domin tabbatar ma duniya cewa, addinin muslunci da addinin yahudawa duk asalinsu guda ne, suna bauta ma Allah daya, kuma shi yana kallon musulmi a matsayin ‘yan uwansa, tare da kiran sauran yahudawa da su san cewa musulmi ba abokan gaba ba ne.

3609053


captcha