Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, Shafin jaridar yanar gizo ta Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, Muhammad
Mukhtar Juma'a minista mai kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana
cewa, danganta addinin musulunci da ayyukan ta'addanci da wasu masu dauke da
akidar kafirta musulmi suke aikatawa, yin hakan babban kure ne.
Ministan ya ce addinin muslunci addini ne da ya zo domin kubutar da rayuwar dan adam da mutuncinsa, saboda haka duk wani abu na kisan dan adam ba gaira ba sabar ko zcin mutuncinsa baya da alaka da muslunci, ko da kuwa mai aikata hakan ya danganta kansa da musulunci.
A daya bangaren ministan ya kirayi malaman addini da cewa su sauke nauyin da ya rataya akansu na wayar da kan musulmi musamman matasa, wadanda su ne aka fi sauran kwasa a duk lokacin da wata guguwa ta zo, domin tabbatar da cewa sun iya banbance mene ne addinin muslunci da koyarwarsa, domin kada su fada cikin kungiyoyin ta'addanci da sunan suna addini.