Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafaqna cewa,
cibiyoyin muslunci da ke karkashin mabiya mazhabar shi'a a birnin London suna
taimaka ma wadanda gobarar ta yi wa yankan kauna.
Ganin cewa da dama daga cikin wadanda abin ya shafa musulmi ne, 'yan shi'a suna shirya musu buda baki tare da gayyatar sauran mutanen da ba msuulmi ba wadanda abin shafa domin su ci abinci tare da sauran msuulmi.
Gobarar wadda ake ganin cewa aiki ne na ganganci, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha bakawai da jikkatar wasu.




