Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,kamfanin dilalncin labaran AP ya bayar da rahoton cewa, Harun Khan
shugaban majalisar musulmin kasar Birtaniya, ya kirayi mahukuntan kasar
da cewa, lokaci ya yi da za su daukin nauyin tabbatar da tsaro a wuraren
ibadar musulmi, maimakon barin su a cikin halin rashin tabbas ta fuskar
tsaro.
Ya ce harin da aka kai ma musulmi yau da sassafe ba shi ne irinsa na farko ba, hakan na faruwa sau da dama a sassa daban-daban na kasar, inda ko mako guda ba ayi ba da cinna wuta akan wani dogon bene da musulmi ne mafi yawan mutanen da suke a cikinsa, a yau kuma an kai musu hari har a wurin ibada a cikin birnin an London.
Ya kara da cewa wadannan abubuwa suna faruwa ne sakamakon karuwar kyamar musulmia tsakanin wasu 'yan kasar ta Birtaniya, alhali musulmin da suke a kasar su ma 'yan kasa ne da suke da dukaknin hakkoki kamar kowane dan kasa, kuma a bisa doka dole ne a kare ma musulmi na hakkokin, tare da basu kariya da kuma tsaron lafiyarsu da kaddarorinsu da mutuncinsu.